Sab Technology

Da sunan Allah mai rahma maijin Qai.

Sunana Muhd Sabiu Yakub A wannan Channel nawa mai suna SAB TECHNOLOGY INSHA ALLAH zan dinga koyar daku ilimin waya da computer dai-dai gwargwadon abinda Allah ya sanar dani.

Ga masu bukatar koyon gyaran waya ko flashing suma ba'a barsu a bayaba, kudai kuyi subscribe ku kasance tare dani akoda yaushe.

Banida buri wanda yawuce naga Al'umar Hausawa munci gaba domin har yanzu mune koma baya a bangaren Technology.

Sannan zan dinga koyar daku Video editing da photo editing ku mallaki application guda biyu kamar haka kinemaster da picsArt akansu zan koyar da komai.

Nasan da yawa cikinku akwai malamaina idan nayi kuskure a dinga yimin gyara kada kubarni da iyawata.

Sannan dan Allah kuyi subscribe idan nasaki video kudinga yimin Like idan kun kalla hakan zaisa naji dadi nadinga yimuku wasu akan lokaci.

Nagode da aramin lokacinku da kukayi Allah (S.W.T) yasaka muku da mafidicin Alkhairi.